La liga

Barcelona zata sanya tutar Catalonia

Mutanen Yankin Catolonia da Tutarsu suna bikin ranar yankinsu a Spain
Mutanen Yankin Catolonia da Tutarsu suna bikin ranar yankinsu a Spain Reuters

Kungiyar Barcelona ta bayyana cewa zata yi amfani da riga mai kalar tutar yankin Catalonia a wasan da kungiyar zata buga a karshen mako a La liga. Wannan matakin kuma ana ganin zai kara harzuka mutanen yankin da ke neman ballewa daga Spain.

Talla

Barcelona tace ta samu tabbaci ne daga hukumar kwallon Spain na neman sauya tufafinta a wasan da zata kara da Bilbao a Nou Camp.

Kungiyar Barcelona tana son karrama yankin ne domin bikin cika shekaru 300 da karbe ikon Barcelona a shekara ta 1714.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI