Wasanni

An dakatar da shugaban Hukumar kwallon Kafa ta kasar Italiya Carlo Tavecchio

Rahotanni daga bangaren wasannin kwallon Kafa na Duniya na cewar an dakatar da shugaban hukumar kwallon Kafa ta kasar Italiya daga shiga harkokin wasanni na Watanni 6 akan zarginsa da nuna wariyar Jinsi

afriksports.com
Talla

Idan ana iya tunawa dai an zabi Carlo a matsayin shugaban hukumar kwallon Kafa ta Italiya ne a cikin watan Agusta, bayan da ya kada abokin karawarsa na AC Milan Demetrio Albertini, amma nada shi a matsayin shugaban ya sa tsohon dan wasar kwallon Kafa na Najeriya wanda a baya ya yi bugawa Club din juventus wasa Sunday Olise, ya ce an yi katobara ga harkokin wasar kwallon Kafa domin Carlos bai cancanci zama shugaba ba lura da yanda yake nuna banbanci.

Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai UEFA ce ta dakatar da shi Carlo Tavecchio dan shekaru 71, domin ya haifar da rikici a lokacin gangamin zabensa a cikin Watan Yuli, inda yake nuna wani yanayi na cin Ayaba idan yana magana akan ‘yan wasar kwallon Kafa na kasashen waje, musamman wadanda suka fito daga Nahiyar Afruka.

Duk da cewar Carlo Tavecchio ya nemi gafara, dakatarwar ta shi ta nuna cewar ba zai samu damar shiga gasar wasannin UEFA mai zuwa bad a za’a yi a cikin Watan Maris na 2015.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI