Ferguson ya amince da sauye sauyen da van Gaal ke yi a United

Tsohon Manajan kungiyar Manchester United, Alex Ferguson
Tsohon Manajan kungiyar Manchester United, Alex Ferguson

Tsohon manajan kungiyar Manchester United, Alex Ferguson ya bayyana goyon bayasa da matakin da Manaja mai ci Louis van Gaal ke shirin dauka, na yiwa jerin ‘yan wasan kungiyar kwaskwarima, ta hanyar kashe makudan kudade a wannan bangaren. United, dake buga wasa a gasar Primiyan kasar Ingila, ta yi hayar Van Gaal ne, don ya wanke daudar da David Moyes ya shafa wa kungiyar, lokacin da aka sa shi ya maye gurbin Ferguson a Old Trafford, inda kungiyar ta taka rawar da ta fi kowacce muni, cikin shekaru 20 da suka gabata.Van Gaal dai yayi ruwan sulalla, da suka haura Fam din Ingila miliyon 150, kwatankwacin Dalar Amurka miliyon 240, inda ya sayo ‘yan wasan da suka hada da Angel di Maria, kan fam miliyon 59, ya kuma sayo su Radamel Falcao da Ander Herrera da Marcus Rojo da kuma Luke Shaw.Yanzu wannan cefanen ‘yan wasan, ya taimakawa kungiyar ta shiga jerin kungiyoyi 4 na farko a a gasar ta Primiya.