Keshi yayi zargin ana mishi zagon kasa a Super Eagles
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Super Eagles ta Nigeria Stephen Keshi, ya ce zagon kasa da ake mishi ne ya sa ‘yan wasan nashi suka sha kashi a hannun ‘yan kasar Sudan, ranar Asabar da ta gabata, yayin wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Africa, da aka yi a birnin Khartoum.Keshi yace abinda yake bashi mamaki shine wadannan ‘yan wasan sune yayi amfani dasu wajen neman shiga gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil a cikin wannan shekarar, kuma su suka lashe gasar cin kofin nahiyar Africa da aka yi a Africa ta Kudu.Wannan shine karo na 3 da ‘yan wasan na Nigeria suka sha kashi a jere, lamarin kuma day a jefa fatan kasar na shiga gasar ta cin kofin Africa da za ayi a kasar Morocco, cikin halin rashin tabbas.