Kwallon kafa

Super Falcons na Nigeria sun yi nasara kan Bayana Bayan na Africa ta Kudu

'Yan kungiyar kwallon kafa ta matan Nigeria, Super Falcons suna atisaye
'Yan kungiyar kwallon kafa ta matan Nigeria, Super Falcons suna atisaye AFP PHOTO / UWE ANSPACH

Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Nigeria wato Super Falcons ta sami nasarar cin ‘yan matan Africa ta Kudu, da ake kira Bayana Bayana ci 2 da 1, a wani wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin mata na Nahiyar Africa, da ake yi a kasar Namibia. Da wannan kungiyar ta Super Falcons ta sami nazarar shiga gasar cin kofin duniya na mata, da za a yi a kasar Canada, a shekara mai zuwa ta 2015Wannan ne karo na 9 da Falcons din ke karawa da Bayana Bayana, kuma a shekaru 2 da suka gabata, ‘yan matan na Nigerai sun sha kashi a hannun ‘yan Africa ta Kudun a daidai wannan matakin wasan na gasar cin kofin mata na Nahiyar Africa, don haka wanan nasara na matsayin daukar fansa.