Kwallon Kafa

Albania ta kalubalanci UEFA

Karabkiyar da aka yi tsakanin Serbia da Albania
Karabkiyar da aka yi tsakanin Serbia da Albania REUTERS/Marko Djurica

Firaministan Albania Edi Rama ya kalubalanci hukumar kwallon Turai UEFA akan hukuncin da hukumar ta yanke na ba kasar Serbia kwallaye uku da banza a wasan da ba’a wanye lafiya ba tsakanin kasashen biyu na yankin Balkans.

Talla

Firaministan na Albania yace hukumar kwallon Turai ta sa siyasa a cikin lamarin, yana mai kalubalantar hukumar akan rashin nuna adalci wajen lura da irin yadda sabiyawa suka yayata kalaman nuna wariya.

A ranar 14 ga watan nan ne na Oktoba ‘Yan kallo a filin Belgrade suka abka wa ‘Yan wasan Albania a fili, bayan wani jirgin sama mai tuka kansa da ya sako da tutar Albania a yayin da suke karawa da Sarbia.

Yanzu haka dai UEFA ta ci kasashen biyu tarar kudi euro dubu dari, sannan nan gaba Albania zata buga wasanninta biyu ba tare da ‘yan kallo ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.