La liga

Barcelona ta sha kashi a gidan Real Madrid

Benzema na Real Madrid ya jefa kwallo a ragar Barcelona
Benzema na Real Madrid ya jefa kwallo a ragar Barcelona Reuters

Real Madrid ta doke Barcelona a fafatawar Clasico ci 3 da 1 a filinta Santiago Bernabeu. Suarez na Barcelona da shi aka fara wasan a karon farko da ya fara haskawa a La liga bayan kawo karshen wa’adin hukuncin watanni hudu da FIFA ta ladabtar da shi saboda tabi’ar cizo.

Talla

Ana fara wasa Neymar ya fara jefa wa Barcelona kwallo a ragar Madrid. Ronaldo da Pepe da Benzema suka zirara kwallaye Real Madrid kwallayenta uku a ragar Barcelona.

Yanzu tazarar maki guda ne Barcelona ta ba Real Madrid a teburin La liga, kafin su sake haduwa a filin Barcelona Nou Camp.

Barcelona ta sha kashi a gidan Real Madrid ci 3 da 1
Barcelona ta sha kashi a gidan Real Madrid ci 3 da 1 REUTERS/Juan Medina

Duk da ya kwashe lokaci ba ya taka kwallo amma Suarez ya yi rawar gani a wasan, domin shi ya ba Neymar kwallon da ya jefa a raga. Sai da aka dawo hutun rabin lokaci ne aka canza Suarez.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI