Faransa

Domenech ya rubuta Kamus din rayuwarsa a Tamola

Raymond Domenech Tsohon Kocin Faransa
Raymond Domenech Tsohon Kocin Faransa GettyImages

Tsohon kocin Faransa Raymond Domenech ya caccaki kocin Chelsea Jose Mourinho da wasu ‘Yan wasan Faransa da ya horar, Franck Ribery da Nicolas Anelka a cikin wani sabon littafinsa da za’a kaddamar a gobe Laraba.

Talla

Littafin wanda Tsohon kocin na Faransa ya kira kamus din rayuwarsa a duniyar Tamola, ya caccaki Mourinho game da taken da ake masa “Translator” Mai fassara.

Haka kuma Raymound yace Anelka shi ne tushen samun baraka a tawagar ‘yan wasan Faransa na rashin nuna da’a musamman a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a kasar Afrika ta kudu.

A cikin Littafin na Domenech ya danganta Henry da Zidane amma yace duk da Henry ya taimakawa Faransa zuwa gasar cin kofin Duniya a 2006 amma darajarsa ta zube a lokacin da ya yi amfani da hannu a karawa tsakanin Faransa da Ireland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.