FIFA

Yaya Toure yana takarar Ballon d’Or

Yaya Touré, nà Manchester City
Yaya Touré, nà Manchester City SOCCER-FINANCES/ REUTERS/Phil Noble/Files

Hukumar FIFA ta fitar da jerin sunayen ‘Yan wasa da za ta zabi gwarzon dan wasan duniya, cikinsu kuma akwai mai rike da kambun Cristiano Ronaldo na Portugal da abokin hamayyarsa Lionel Messi na Argentina. Akwai kuma ‘Yan kasar Jamus guda shida da suka lashe gasar cin kofin duniya a Brazil.

Talla

Yaya Toure na Cote d’Ivoire daga Afrika wanda ke taka kwallo a Manchester City yana cikin jerin sunayen da FIFa ta ware domin zaben gwarzon dan wasan duniya.

‘Yan wasa kusan 10 ne a gasar La liga ta Spain aka zaba cikin jerin sunayen da za’a zabi gwarzon dan wasa na FIFA, sai dai cikinsu babu mai tabi’ar cizo Luis Suarez na Barcelona.

Gareth Bale (Wales)

Karim Benzema (Faranse)

Diego Costa (Spain)

Thibaut Courtois (Belgium)

Cristiano Ronaldo (Portugal)

Angel Di Maria (Argentina)

Mario Goetze (Germany)

Eden Hazard (Belgium)

Zlatan Ibrahimovic (Sweden)

Andres Iniesta (Spain)

Toni Kroos (Jamus)

Philipp Lahm (Jamus)

Javier Mascherano (Argentina)

Lionel Messi (Argentina)

Thomas Mueller (Jamus)

Manuel Neuer (Jamus)

Neymar (Brazil)

Paul Pogba (Faransa)

Sergio Ramos (Spain)

Arjen Robben (Netherlands)

James Rodriguez (Colombia)

Bastian Schweinsteiger (Jamus)

Yaya Toure (Cote d’Ivoire).

A farkon watan Disamba ne hukumar FIFa zata ware sunayen ‘Yan wasa uku domin bayyana sunan gwarzo daga cikinsu a ranar 12 ga watan Janairu a birnin Zurich.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.