Kwallon Kafa

FIFA ta ba Najeriya wa’adi

Tambarin Hukumar kwallon Najeriya NFF
Tambarin Hukumar kwallon Najeriya NFF

Hukumar FIFA da ke kula da sha’anin kwallon kafa a duniya ta ba Najeriya wa’adi daga nan zuwa ranar juma’a, a dawo da kwamitin zartawar hukumar kwallon kafar kasar NFF da kotu da tube, in ba haka ba kuma FIFA ta dakatar da Najeriya.

Talla

An dai kwashe kusan tsawon watanni hudu ana rikici a hukumar kwallon Najeriya. Kuma a makon jiya ne wata kotu a kasar ta dakatar da su Amaju, bayan su Chris Giwa sun shigar da kara.

Giwa dai yana ikirarin shi ne shugaban NFF wanda aka zaba a ranar 26 ga watan Agusta, amma FIFA ba ta amince da shi ba, lamarin da ya sa ya shigar da kara.

FIFA ta dade tana gargadin Najeriya, kuma a cikin wata wasika zuwa ga Amaju, wanda aka zaba shugaban NFF a ranar 30 ga watan Satumba, FIFA ta tsawaita wa’adi ga Najeriya har zuwa Juma’a in ba haka ba kuma hukumar za ta dauki mataki akan Najeriya mai tsauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.