Messi ya kafa tarihi a La liga
Wallafawa ranar:
Lionel Messi ya kafa tarihi a gasar La liga a Spain a karshen mako a matsayin wanda ya fi yawan zira kwallaye a tarihin gasar bayan ya jefa kwallaye uku a raga inda Barcelona ta doke Sevilla ci 5-1.
Lionel Messi ya sadaukar da tarihin da ya kafa ga abokan wasan shi a Barcelona bayan ya zama wanda ya fi zirara kwallaye a raga 253 a gasar La liga.
Messi ya kafa tarihin ne a ranar Assabar bayan ya jefa kwallaye uku a ragar Sevilla inda ya sha gaban tsohon gwanin raga a gasar Telmo Zarra.
Real Madrid kuma ta lallasa Eibar ne ci 4-0, kuma karo 14 ke nan Real Madrid na karawa ba tare da samun galaba akanta ba. Cristiano Ronaldo ne ya zirara kwallaye biyu a raga.
Har Yanzu Real Madrid ce saman teburin La liga da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona da ke matsayi na biyu.
Atletico Madrid mai rike da kofin La liga ta doke Malaga ne ci 3-1 kuma tazarar maki hudu ne tsakaninta da Real Madrid.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu