Zakarun Turai

Di Matteo zai hadu da Mourinho, Messi zai kafa tarihi

Roberto Di Matteo na  Schalke 04 .
Roberto Di Matteo na Schalke 04 . REUTERS/Ina Fassbender

Roberto Di Matteo zai hadu da Jose Mourinho a karawa tsakanin Chelsea da Schalke 04 a gasar Zakarun Turai da za a ci gaba da fafatawa a yau Talata. Di Matteo shi ya fara lashewa Chelsea kofin Zakarun Turai a tarihin kungiyar a 2012 kafin ta raba gari da shi.

Talla

Di Matteo zai karbi bakuncin Chelsea ne a matsayin kocin Schalke 04. Kuma Di Matteo ya ce babu adawa illa zai yi fatar ‘yan wasan shi su doke Chelsea.

Chelsea na iya tsallakewa zagaye na gaba a gasar a yau idan ta samu sa’a, kodayake a karawa ta farko sun tashi kunnen doki ne da Schalke 04 a Stamford Bridge kafin Di Matteo ya karbi aikin horar da kungiyar.

Tun da farko ne CSKA Moscow da Roma zasu fara kece raini a kasar Rasha kafin sauran wasannin.

Manchester City za ta fafata ne da Bayern Munich a Ingila, inda dole sai City ta doke Munich kafin tunanin tsallakewa zuwa zagaye na gaba a gasar.

A kwanan baya Manchester City ta sha kashi ne ci 2 da 1 a hannun CSKA Moscow, kuma yanzu ita ke kasan rukuninsu da maki biyu. Tuni Bayern Munich ta tsallake a rukunin.

Barcelona da PSG wadanda tuni suka tsallake a rukuninsu na F, dukkaninsu za su yi fafutikar samun nasara ne a wasannin da za su fafata a yau domin jagorancin rukunin.

PSG da ke jagorancin teburin rukunin da maki 10 za ta karbi bakuncin Ajax ne a Paris. Barcelona da ke matsayi na biyu da maki 9 za ta zai wa APOEL ziyara ne a Cyprus.

Barcelona na bukatar maki guda ne ta karbe ragamar jagorancin rukunin, domin kaucewa haduwa da wata babbar kungiya a zagaye na gaba.

TARIHIN MESSI

Wani batu kuma da zai ja hankali a gasar Zakarun Turai shi ne tarihin da Messi zai sake kafawa a Turai domin zama wanda ya fi zirara kwallaye a gasar bayan ya zama limamin raga a gasar La liga ta Spain a karshen mako.

'Yan wasan Barcelona suna taya Messi murnar zama shugaban raga a Spain bayan ya jefa kwallaye 3 a ragar Sevilla wanda ya ba shi jimillar kwallaye 253 a La liga
'Yan wasan Barcelona suna taya Messi murnar zama shugaban raga a Spain bayan ya jefa kwallaye 3 a ragar Sevilla wanda ya ba shi jimillar kwallaye 253 a La liga REUTERS/Albert Gea

Messi ya jefa kwallaye 253 a La liga.

Makwanni uku da suka gabata ne Messi ya yi kafada da Raul tsohon dan wasan Real Madrid da ya jefa kwallaye 71 a gasar zakarun Turai.

A yau kuma Messi na iya shan gabansa idan har ya jefa kwallo a raga.

A ranar juma’a ne dai za’a rufe kada kuri’ar zaben gwarzon dan wasan duniya, inda Messi ke harin lashe kyautar karo na biyar, duk da cewa yana takara da Cristiano Ronaldo na Real Madrid mai rike da kambun kuma wanda ya lashe gasar zakarun Turai da kofin Sarki a Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI