Kwallon Kafa

Henry ya fice New York Red Bulls

Thierry Henry dan wasan New York Red Bulls
Thierry Henry dan wasan New York Red Bulls REUTERS/Mike Cassese

Tsohon dan wasan Arsenal da Barcelona Thierry Henry na Faransa ya fice New York Red Bulls ta Amurka bayan shafe shekaru kusan hudu da rabi yana taka kwallo a gasar Major League Soccer. Henry yace lokacin yin bakwana da kungiyar ne ya yi bayan cikar wa’adin kwangilar shi da New York Red Bulls.

Talla

Dan wasan yace zai dan sarara nan da makwanni kafin sanin makomar shi a harakar tamola.

A kwanan baya Henry ya kwarmata wata jaridar Faransa cewa yana fatar komawa Arsenal domin fara aikin horar da ‘yan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.