Kwallon Kafa

Boateng yana son zama Kaftin na Jamus

Kaerim Benzema na Faransa yana fafatawa da Jerome Boateng na Jamus
Kaerim Benzema na Faransa yana fafatawa da Jerome Boateng na Jamus REUTERS/Kai Pfaffenbach

Dan wasan Bayern Munich Jerome Boateng yace yana fatar zama Kaftin na Jamus anan gaba a matsayin bakar fata na farko da zai jagoranci ‘yan wasan kasar. Bastian Schweinsteiger ne jagora yanzu bayan Philipp Lahm ya yi ritaya, amma Boateng yace anan gaba yana fatar zama kaftin na Jamus.

Talla

Boateng wanda dan asalin kasar Ghana ne, ya yi wa Jamus haskawa 50 a wasanninta tun haskawarsa ta farko a 2009.

Kuma dan wasan ya taba daura damarar Kaftin a hannu a lokacin wasan sada zumunci tsakanin Jamus da Argentina a 2012.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.