Olympics

Kasashe biyu na iya daukar nauyin Olympics

Tambarin wasannin Olympics
Tambarin wasannin Olympics REUTERS/David Gray

Kwamitin shirya wasannin Olympics ya kada kuri’ar amincewa da matakin ba kasashe biyu damar daukar nauyin gudanar da wasannin tare da kuma bude kofar shigar da wasu sabbin wasanni a Olympics.

Talla

Hakan dai na nufin kasashe za su samu saukin neman karbar bakuncin wasannin, tare da kuma jan hankalin al’umma ga wasannin na Olympics da ake gudanarwa a lokacin hunturu da bazara.

Sabbin sauye sauye guda 40 ne shugaban hukumar IOC ya gabatar wanda sauran mambobin za su amince tsakanin yau Litinin zuwa gobe Talata a birnin Monaco.

Sabon tsarin zai ba kasashe biyu da za su karbi bakuncin gasar damar shigar da wasu sabbin wasanni, amma dole sai hukumar shirya wasannin ta amince.

Wata kila nan gaba wasannin al’adun hausawa irinsu Kokuwa da Dambe da Langa su iya shiga wasannin Olympics idan har Nijar ko Najeriya ko wasu kasashen yammacin Afrika suka samu damar karbar bakuncin wasannin.

Yanzu haka Japan da za ta karbi bakuncin wasannin na Olympics a 2020 tana neman a saka wasan Baseball da wani wasan mai kama da Baseball da ake kira Softball.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.