Kwallon Kafa

Manchester ta dawo matsayi na uku a Firimiya

Van Parsie yana murnar zira kwallo a ragar Southampton a filin wasa na St Mary
Van Parsie yana murnar zira kwallo a ragar Southampton a filin wasa na St Mary REUTERS/Andrew Winning

Kungiyar Manchester United ta dare zuwa matsayi na uku a teburin gasar Firimiya ta Ingila bayan ta doke Southampton ci 2 da 1 a karawar da suka yi a daren litinin. Robin van Persie ne ya kwaci Manchester a St Mary da maki uku, wanda ya ba kungiyar nasarar tsallakawa zuwa matsayi na uku a tebur tare da datse yawan makin da ke tsakaninta da Chelsea.

Talla

Yanzu karo na biyar ke nan a jere Manchester na samun nasara, kafin ranar Lahadi ta karbi bakuncin Liverpool a Old Trafford.

Matar Radamel Falcao na Manchester ta mayar wa kocin kungiyar Louis van Gaal da martani bayan yace mijinta minti 20 kacal ya ke iya yin wasa bayan ya murmure daga raunin da ya ji.

Kocin na Manchester yace har yanzu Falcao bai murmure ba domin yana bukatar lokaci.

Amma Matar dan wasan ta yi watsi da ikirarin na Van Gaal tana mai cewa ya murmure dari bisa dari kamar yadda ta sako hotonsu suna murmushi a Instgram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.