Kwallon Kafa

United na iya karbe teburin Firimiya-Rooney

Wayne Rooney na Manchester United
Wayne Rooney na Manchester United REUTERS/Nigel Roddis

Wayne Rooney yace Manchester United na iya karbe teburin Premier daga hannun Chelsea ganin yadda suka samu nasara a wasanni shida da suka buga . A ranar Lahadi ne Manchester United ta lallasa Liverpool ci 3-0 a Old Trafford, kuma duk da cewa Manchester ta sha wahala a farko Firimiya.

Talla

Yanzu haka kuma tazarar maki 8 ne Chelsea ta ba United, kuma Rooney ya ce idan dai har zasu samu nasara a wasanninsu to komi na iya faruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.