Bundesliga

Robben ya jefawa Bayern Munich kwallo 100 a raga

Arjen Robben na Bayern Munich
Arjen Robben na Bayern Munich REUTERS

Arjen Robben ya jefa wa Bayern Munich kwallon shi ta 100 a raga, inda ya taimakawa kungiyar doke Freiburg ci 2da 0 a jiya Talata. Yanzu tazarar maki 12 ne Bayern Munich ta ba Wolfsburg a teburin Bundesliga, kafin Wolfsburg ta yi kokarin datse maki uku idan ta samu nasara a karawarta da Borussia Dortmund a yau Laraba.