Kwallon Kafa

Masar ta amince a shiga kallon wasanni

Rikici tsakanin magoya bayan  Al Ahly da Al Masry a Port Said na Masar
Rikici tsakanin magoya bayan Al Ahly da Al Masry a Port Said na Masar

Hukumar kwallon kafa a kasar Masar ta ba masoya kwallon kafa damar shiga kallon wasu wasannin Lig din kasar wanda shi ne karon farko tun kazamin rikicin da aka samu a filin wasa a 2012.

Talla

Sai dai kuma har yanzu hukumar ta haramta shiga kallon wasannin manyan kungiyoyin kwallon kafar kasar guda shida da suka hada da Al-Ahly, da Zamalek da Al-Ittihad da Al-Masry wadanda za su ci gaba da buga wasanninsu ba tare da ‘yan kallo ba.

Haka kuma hukumar ta takaita adadin magoya bayan kungiyoyin da zasu shiga kallon wasannin.

Kasar Masar dai ta haramtawa magoya bayan kungiyoyin kwallo kafa a kasar shiga kallon wasanni sakamakon wani mumunan rikici da ya faru a watan Fabrairun 2012 a Port Said a lokacin da Al Masry da Al Ahly ke fafatawa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 74.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.