Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Atletico ta karbo Torres

Fernando Torres.
Fernando Torres. REUTERS/Javier Barbancho
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 Minti

Kungiyar AC Milan ta ba Atletico Madrid aron Fernando Torres tsohon dan wasanta da Liverpool da Chelsea. A yarjejeniyar da kungiyoyin biyu suka kulla Torres zai bugawa Atletico kwallo har zuwa karshen kakar 2015 zuwa 2016.

Talla

AC Milan ta karbo Torres ne daga Chelsea amma Tun zuwan Torres a AC Milan kwallon guda ya jefa a raga.

Chelsea ta saye Torres ne Fam Miliyan 50 daga Liverpool amma yanzu Atletico Madrid ta tabbatar da karbar aron dan wasan a shafinta na Intanet.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.