Spain

Barcelona ta sallami Zubizarreta

Zubizarreta na Barcelona
Zubizarreta na Barcelona facbarcelona

Kungiyar Barcelona ta sallami daraktan wasanninta Andoni Zubizarreta, haka kuma mataimakinsa Carles Puyul ya yi murabus. Babu wani bayani da Barcelona ta bayar kan dalilin korar Zubizarreta wanda tsohon gwalkifanta ne a tsakanin shekarun 1986 zuwa 1994.

Talla

Matakin na zuwa ne bayan Real Sociedad ta ba Barcelona kashi ci 1 da 0 da kuma haramcin sayen ‘yan wasa da kotun wasanni ta yi watsi da koken Kungiyar.

Yanzu dai sai a watan Janairu ne Barcelona za ta saye ‘Yan wasa bayan FIFA ta kakaba mata takunkumi saboda keta dokar sayen matasa ‘yan kasa da shekara 18 a watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.