Kwallon Kafa

Maradona yana son Neuer ya lashe Ballon D’Or

Golan kasar Jamus Manuel Neuer
Golan kasar Jamus Manuel Neuer REUTERS/David Gray

Tsohon fitataccen dan wasan Argentina Diego Maradona yace Manuel Neuer na Jamus ne ya cancanta ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya fiye da zaratan da ke takara da shi Cristiano Ronaldo na Portugal da Lionel Messi na Argentina.

Talla

Maradona ya fadi ra’ayinsa ne a kasar Cuba, kuma tsohon dan wasan na Argentina ya ce Neuer ne ya makata ya zama gwarzon duniya saboda shi ya lashe kofin duniya a Brazil.

Cristiano Ronaldo ne ke rike da kambun kuma ya fi Messi kwarin guiwar lashe kyautar wanda ya karbi Ballon D’Or har sau hudu.

A ranar 12 ga watan Janairu ne FIFA za ta bayyana sunan gwarzo a bana tsakanin Neuer da Messi da Ronaldo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.