FIFA

Yarima Ali na Jordan zai kalubalanci Blatter

Yarima  Ali Bin Al-Hussein Mataimakin shugaban FIFA a yankin Asia
Yarima Ali Bin Al-Hussein Mataimakin shugaban FIFA a yankin Asia Wikipedia

Yarima Ali na Jordan ya bayyana cewa zai kalubalanci Sepp Blatter a zaben shugabancin hukumar FIFA da za a gudanar a nan gaba cikin shekarar 2015. Yarima Ali Bin Al Hussian wanda mataimakin Blatter ne a yankin Asia ya fadi a shafin Twitter cewa zai tsaya takarar shugabancin hukumar FIFA.

Talla

A cewarsa ya yanke shawarar tsayawa takara ne bayan wasu manyan jami’an kwallon kafa sun nemi ya tsaya.

FIFA dai na fama da rikicin rashawa musamman badakalar ba Qatar da Rasha nauyin daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 da 2022.

Yarima Ali yana cikin manyan Jami’an FIFA da suka nemi a wallafa rahoton binciken da aka gudanar kan ba Qatar da Rasha nauyin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.