Kamaru

Song ya yi wa Kamaru ritaya

Dan wasan Kamaru Alexandre Song
Dan wasan Kamaru Alexandre Song AFP PHOTO / JAVIER SORIANO

Dan wasan Kamaru Alex Song ya bayyana yin ritaya daga bugawa kasarsa kwallon kafa bayan cire sunansa daga cikin jerin ‘yan wasan da zasu wakilci kasar a gasar cin kofin Afrika da za a gudanar a kasar Equatorial Guinea.

Talla

Song yana cikin ‘yan wasan Kamaru da suka je gasar cin kofin duniya a Brazil kuma tun lokacin da aka ba shi jan kati a karawar Kamaru da Croatia bai sake bugawa Kamaru kwallo ba.

Song ya fadi a cikin sakon da ya aiko a Instagram cewa ya yi ritaya, tun da an ajiye shi daga shiga gasar cin kofin Afrika.

A ranar 17 ga watan Janairu ne dai za a bude wasannin gasar cin kofin Afrika, a kammala 8 ga watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.