Kwallon Kafa

Chelsea ta yi watsi da batun Messi

Lionel Messi na Barcelona wanda ya kafa tarihin zama malamin raga a gasar zakarun Turai
Lionel Messi na Barcelona wanda ya kafa tarihin zama malamin raga a gasar zakarun Turai Reuters

Kungiyar Chelsea ta yi watsi da jita-jitar da ake yi cewa za ta saye Messi bayan dan wasan ya ja hankalin jama’a a lokacin da ya fara bibiyar shafin kungiyar na Istagram. Wannan kuma ya biyo bayan takun sakar da Messi ke yi da kocin Barcelona Luis Enrique.

Talla

Mataimakin mai horar da ‘yan wasan Chelsea Steve Holland ya yi watsi da cewa kungiyar za ta saye Messi akan kudi da suka haura Fam Miliyan 200.

Mataimakin na Mourinho ya ce duk da lura da cewa Chelsea tana da arzikin sayen Messi amma darajar kudin da aka saka wa dan wasan ya keta dokokin cinikin ‘yan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.