Ballon d'Or

Cristiano Ronaldo ya sake zama gwarzon duniya

Cristiano Ronaldo na Real Madrid yana karbar kyautar gwarzon duniya daga hannun Shugaban FIFA  Jospeh Blatter.
Cristiano Ronaldo na Real Madrid yana karbar kyautar gwarzon duniya daga hannun Shugaban FIFA Jospeh Blatter. REUTERS/Ruben Sprich

Cristiano Ronaldo na Real Madrid ne gwarzon dan wasan duniya wanda ya sake karbar kyautar a jiya Litinin a bikin da FIFA ta gudanar a birnin Zurich. Karo na uku ke nan da Cristiano Ronaldo ke lashe kyautar.

Talla

Ronaldo na Portugal ya doke Lionel Messi ne na Argentina da Manuel Neuer na Jamus.

Cristinao ya lashe kyautar ne da kuri’u sama da kashi 37 da masu horar da ‘yan wasa a kasashe 181 suka jefa da kuma kaftin kaftin da ‘Yan jaridu na kasashen.

Messi ne a matsayi na biyu, yayin da kuma Neuer ya zo a matsayi na uku.

Ronaldo ya lashe kyautar ne bayan ya taimakawa Real Madrid lashe kofin zakarun Turai karo na 10, bayan shafe shekaru 12 kungiyar na yunwar kofin.

Sannan shi ne ya fi zirara kwallaye a gasar a kakar da ta gabata, kodayake a zagayen Farko aka yi waje da tawagar shi ta Portugal a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Kocin kasar Jamus Joachim Loew aka ba gwarzon koci, wanda ya taimakawa kasar Jamus lashe kofin duniya a Brazil.

Loew ya doke Carlo Ancelotti ne na Real Madrid da kuma Diego Simeone na Atletico Madrid.

Dan wasan kasar Colombia ne James Rodriguez ya karbi kyautar wanda kwallon shi ta fi shahara a raga a 2014, wanda ya doke Robin van Persie da jarumar Ireland Stephanie Roche.

Rodriguez ya jefa kwallon ne a ragar Uruguay a gasar cin kofin duniya a Brazil

Nadine Kessler ta Wolfsburg ta karbi kyautar jaruma ta duniya. Kocinta ne Ralf Kellermann aka ba gwarzon kocin Mata.

Akwai wani tsohon dan Jaridar kasar Japan Hiroshi Kagawa mai shekaru 89 da ya karbi kyautar shugaban FIFA, wanda sau 10 yana ziyartar gasar cin kofin duniya domin aiko da rahotanni.

Kungiyar FIFA.

A cikin tawagar FIFA babu dan wasa daga Ingila, ‘Yan wasan Bundesliga da La liga ne suka mamaye tawagar.

Manuel Neuer na Bayern Munich, Sergio Ramos na Real Madrid, Thiago Silva na Paris Saint Germain, David Luiz na Paris Saint Germain, Philipp Lahm na Bayern Munich, Andrés Iniesta na Barcelona, Toni Kroos Real Madrid, Ángel Di Maria na Manchester United, Arjen Robben na Bayern Munich, Lionel Messi na Barcelona, Cristiano Ronaldo na Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.