Messi yana iya ficewa Barcelona
Wallafawa ranar:
Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya nuna cewa yana iya ficewa Barcelona anan gaba. Messi ya shaidawa manema labarai bayan kammala bikin bayar da kyautar gwarzayen duniya a birnin Zurich cewa bai san yadda makomarsa za ta kasance ba a shekara mai zuwa.
A makon daya gabata batun Messi ya mamaye kanun labaran wasanni bayan jita-jitar zai fice Barcelona zuwa Chelsea ko Manchester City saboda sabani tsakanin shi da mai horar da Barcelona Luis Enrique.
Sau hudu Messi na lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya a jere da jare a Barcelona amma ya jaddada cewa zai ci gaba da rayuwa a Barcelona, kamar yadda bai san makomarsa ba anan gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu