Asia

Iran da Daular Larabawa sun kai Kwata Fainal

Magoya bayan kasar Iran
Magoya bayan kasar Iran

Kasashen daular Larabawa da Iran sun tsallake zuwa gzayen kwata fainai a gasar cin kofin Asia da ke gudanar a Australia. Ana fara wasa da dakika 14 dan wasan Daular Larabawa Ali Mabkhout ya jefa kwallo a ragar Bahrain wanda shi ne lokaci mafi kanknata a tirihin gasar da wani dan wasa ya zira kwallo a raga.

Talla

Daular larabawa ta shiga zagayen kwata fainal ne bayan ta doke Bahrain ci 2-1. Iran kuma ta doke Qatar ne ci 1-0 a yau Alhamis.

Dole sai Qatar ta samu nasara a wasanta na gaba kafin ta tsallake a zagaye na gaba bayan ta sha kashi a gun Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.