Ingila

Liverpool ta rike Chelsea

John Obi Mikel na Chelsea a karawarsu da Liverpool
John Obi Mikel na Chelsea a karawarsu da Liverpool REUTERS/Phil Noble

Liverpool ta yi kunnen doki da Chelsea a karawa ta farko da suka fatawa a zagayen dab da na karshe a League Cup. Raheem Sterling ne ya rama wa Liverpool kwallon da Eden Hazard na Chelsea ya jefa a raga a bugun fanariti. Nan gaba kungiyoyin biyu za su sake haduwa a Stamford Bridge.

Talla

Duk dai wanda ya samu nasara tsakaninsu zai hadu ne da Tottenham ko Sheffield United wadanda za su kece raini a yau Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.