CAN 2015

Eq Guinea da Congo sun kai Kwata Fainal

Equatorial Guinea na fafatawa da Congo a Bata
Equatorial Guinea na fafatawa da Congo a Bata Reuters/Mike Hutchings

Kasar Equatorial Guinea da Congo Brazzaville sun tsallaka zagayen kwata fainal a rukuninsu na A a gasar cin kofin Afrika da Equatorial Guinea ke daukar nauyi. Congo ta tsallake ne bayan ta doke Burkina Faso ci 2 da1, yayin da kuma Eq Guinea ta lallasa Gabon ci 2 da 0.

Talla

Karo na bakwai ke nan da Congo Brazaville ke shiga zagayen Kwata Fainal amma wannan ne karo na farko tun 1992 a tarihin gasar Afrika.

A yau Litinin ne kuma kasashen da ke rukunin B za su fafata, inda Tunisia za ta kara da Jamhuriyyar Congo, Zambia kuma ta kece raini da Cape Varde.

Tunisia dai tana neman maki guda ne kacal, yayin da kuma dole sai Zambia ta doke Cape Verde kafin ta samu damar tsallakewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.