Tennis

Serena da Wawrika sun kai zagayen kwata fainal a Australian Open

Serena Williams Jarumar Tennis ta Amurka
Serena Williams Jarumar Tennis ta Amurka REUTERS/Carlos Barria

Mai rike da kambun gasar Austrilan Open Stanilas Wawrinka ya kai ga shiga zagayen Kwata Fainal bayan ya doke Guillermo Garcia-Lopez a fafatawar da suka yi a yau Litinin. Nan gaba zai hadu ne da Kri Nishikori na Japan wanda ya doke David Ferrer na Spain.

Talla

Jarumar Tennis ta duniya Serena Williams ta tsallake zuwa zagayen kwata fainal a gasar Australian Open bayan ta doke Garbine Muguruza ta Spain.

Dominika Cibulkova ta Slovakia ta yi waje da Victoria Azarenka ta Belerus a yau Litinin.

Yau ne aka shiga kwanaki na 8 a gasar da ake gudanarwa a Melbourne. Kuma a yau Novak Djokovic zai fafata da Gilles Muller na Luxembourg.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.