Tennis

Berdych ya doke Nadal

Rafael Nadal
Rafael Nadal REUTERS/Carlos Barria

Tomas Berdych ya yi waje da Rafeal Nadal a gasar Australian Open da suka fafata a yau Talata a birnin Melbourne zagayen kwata Fainal. Berdiych a bana ya samu sa’ar nadal bayan sau 17 yana shan kashi a hannunsa tun 2006. Maria Sharapova ta doke Eugenie Bouchard a gasar zagayen kwata fainal.

Talla

Makarova ma ta doke Simona Halep. Serena kuma za ta kara ne da Dominika Cibulkova a gobe Laraba.

A bana Serena za ta iya haduwa da ‘yar uwarta Venus Williams a zagayen kusa da karshe idan sun tsallake, wanda shi ne karo na farko tun 2000 da jaruman Tennis din suka hadu da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.