Messi ya yi ruwan kwallaye uku a ragar Lavente
Wallafawa ranar:
Lionel Messi ya yi ruwan kwallaye uku a raga a jiya Lahadi inda Barcelona ta casa Levente ci 5 da 0. Kuma Messi ya jefa kwallayen ne a lokacin da ya ke yin bikin haskawa karo 300 a gasar La liga.
Karo na 31 ke nan Messi na jefa wa Barcelona kwallaye uku a raga yayin da a yanzu ya yi kafada da Talmo Zerra.
Neymar da Suarez ne suka jefa wa Barcelona sauran kwallayenta a ragar Lavente.
Tun a ranar Assabar ne Real Madrid ta doke Deportivo la Coruna ci 2 da 0.
Karo 11 ke nan da Barcelona na samun nasara a jere da jere.
Har yanzu tazarar maki guda ne Real Madrid ta ba Barcelona a teburin La liga.
Atletico Madrid ta sha kashi ne ci 2 da 0 a hannun Celta Vigo a jiya Lahadi. Yanzu maki 7 ne ke tsakaninta da Madrid a teburin La Liga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu