Zakarun Turai

Monaco ta doke Arsenal

Dimitar Berbatov na Monaco yana wanda ya zira kwallo a ragar Arsenal.
Dimitar Berbatov na Monaco yana wanda ya zira kwallo a ragar Arsenal. Reuters / John Sibley Livepic

Monaco ta bi Arsenal har gida Ingila ta doke ta ci 3 da 1 a gasar zakarun Turai. A daya bangaren kuma Bayer Leverkusen ta doke Atletico Madrid ci 1 da 0 a Jamus, amma kocin Atletico Diego Simeone yace har yanzu wasa bai kare ba har sai an fafata a karawa ta biyu.

Talla

Tun loakcin da aka hada kungiyoyi biyu, ake hasashen Arsenal ta samu bagas akan tana iya korar Monaco a gasar, amma “Dan hakin da ka raina, shi ke tsone maka ido”

Arsenal na kan hanyar ficewa gasar a karo na biyar ba tare da tsallakewa zuwa zagayen kwata fainal ba, sakamakon kashin da ta sha a Emirate.

A karawa ta biyu Arsenal sai ta yi da gaske a gidan Monaco domin sauya sakamakon wasan.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya mika lafin ga ‘yan wasan shi na baya wadanda suka bari aka jefa masu kwallaye a raga.

A daya bangaren kuma Bayer Leverkusen ta doke Atletico Madrid ci 1 da 0 a Jamus, amma kocin Atletico Diego Simeone yace har yanzu wasa bai kare ba har sai an fafata a karawa ta biyu.

Leverkusen dai na son tsallakewa ne zuwa zagayen kwata fainal a karon farko tun 2002 da ta buga wasan karshe a gasar zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI