Wasanni

Arsene Wenger ya ce Monaco bata cancanci matsayinta ba

Arsène Wenger, meneja wa Arsenal.
Arsène Wenger, meneja wa Arsenal. Reuters

Manajan Arsenal Arsene Wenger da ya ce Monaco bata cancanci matsayinda take akai ba na shiga matsayin buga wasar ta kusa da ta kusa da ta karshe a gasar cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai

Talla

Wenger na bada amsar tambayar da aka yi masa ne cewar yana ganin Monaco ta cancanci matsayinta, “ya ce baya tunanin hakan musamman idan aka lura da yawan Maki na haura kwallo da suke da shi” Ya ce duk sa’adda aka lallasa Club dinka za ka ji ba dadi, amma a wannan karon kam a nashi gani basu rasa matsayinsu ba.

Amma fa kalaman na Wenger sun yi takon saka da na Captain din Club din na Arsenal Per Mertesacker, da ya ce sun yi nadamar wasar su ta farko.

Kalama nasi na zuwa ne bayan da aka buga wasanni tsakanin Atlantiko Madrid da Bayer Levkn inda Madrid ta lallasa Bayern da ci 1 mai ban haushi.

Sai kuma Monaco da ta sha kashi ga hannun Arsenal 2 – 0, amma kuma sakamakon ya nuna Monaco ce ta samu nasara, wanda shi ne musabbabin wadancan kalaman da Arsene Wenger ke fada.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.