Wasanni

FIFA ta maida hankali ga batun wariyar launin fata na kasar Rasha

Hukumar kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta maida hankali ga shawo kan matsalar wariyar launin fata a kasar Rasha a bangaren wasannin kwallon kafa, a yayin da ake fuskantar gasar cin Kofin Duniya na 2018

Talla

Shugaban hukumar yaki da wariyar launin fata Jeffrey Webb, ya ce matsalar ta kasar Rasha na damuwar harkokin wasanni a Duniya, amma kuma ga alama, Rasha ta hankalta da wannan kuma za su yi aiki da ita domin maganin wannan matsalar.

Matasalar wariyar launin fata a fannin wasanni dai babbar matsala ce, kuma dai daga cikin matsalolin da ke tada jijiyoyin wuya a tsakanin Clublikan wasannin kwallon kafa da kuma Hukumomin kula da harkokin wasanni, abinda ke saka hukumomin daukar matakan maganceta.

Akasari wannan matsalar ta fi faruwa ne tsakanin ‘yan wasar Afruka, da kuma na yankin Nahiyar Turai, ko gabas ta tsakiya, harma da Asiya
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.