Tennis

Serena ta samu nasara a wasanni 700

Serena Williams
Serena Williams REUTERS/Issei Kato

Jarumar Tennis ta duniya Serena Williams ta doke Sabine Lisicki ta Jamus ci 7 da 6 (7 da 4), 1 da 6, 6 da 3 a jiya Laraba wanda ya bata damar tsallakewa zuwa zagayen kusa da karshe a gasar Miami Masters. A jiy Serena ta samu nasara karo na 700 a rayuwarta a Tennis.

Talla

Nan gaba Serena za ta hadu ne da Simona Halep ta Romania Sloane Stephen domin neman tsallakewa zuwa zagayen karshe wacce ta doke

‘Yan wasan biyu sun taba haduwa a zagayen dab da na karshe a Indian Wells amma Serena ta fice wasan saboda rauni wanda ya ba Helep nasarar lashe kofin gasar bayan ta doke Jelena Jankovic a zagayen karshe

Maza

Andy Murray na Birtaniya zai kara ne da Tomas Berdych na Jamhuriyar Czech a zagayen dab da na karshe a Miami bayan ya doke Dominic ci 3 da 6, 6 da 4 da 6 da 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.