La liga

Messi ya murmure

Lionel Messi na Barcelona  ya kafa tarihin zama malamin raga a gasar zakarun Turai
Lionel Messi na Barcelona ya kafa tarihin zama malamin raga a gasar zakarun Turai Getty Images

Kungiyar Barcelona tace Lionel Messi ya murmure kuma zai iya buga wasan da kungiyar za ta kece raini da Celta Vigo a karshen mako nan, bayan dan wasan ya yi jinya na ‘yan kwanaki wanda ya sa ya kauracewa wasannin sada zumunci da kasar shi Argentina ta doke El Salvador da kuma Ecuador.

Talla

Messi ya samu rauni a wasan Clasico da Barcelona ta doke Real Madrid ci 2 da 1, amma a jiya Alhamis dan wasan ya fito horo a Barcelona.

Hanzu Barcelona ce ke jagorancin teburin La liga akan Real Madrid yayin da ya rage saura wasanni 7 a kammala gasar.

A ranar Lahadi ne Real Madrid za ta kara ne da Granada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI