La liga

Alves zai fice Barca

Dani alves Dan wasan Barcelona lokacin da ya ke zantawa da manema Labarai game da gasar Zakarun Turai da zasu kara da kungiyar Bayer Leverkusen a kasar Jamus
Dani alves Dan wasan Barcelona lokacin da ya ke zantawa da manema Labarai game da gasar Zakarun Turai da zasu kara da kungiyar Bayer Leverkusen a kasar Jamus

Alamu na nuna cewa Dani Alves na Brazil na kan hanyar ficewa Barcelona bayan ya ki amincewa da tayin da kungiyar ta yi masa na tsawaita kwantaraginsa idan kwangilar shi ta kawo karshe. Yanzu haka manyan kungiyoyin Turai na neman dan wasan da suka hada da PSG da Manchester United.

Talla

Wakilinsa Dinorah Santana ya ce lura da yadda dan wasan ke buga wa Barcelona wasa a ko yaushe, yana bukatar karin kudade fiye da yadda ya ke karba a yanzu.

Kofuna 16 Alves ya lashe a Barcelona tun zuwansa daga sevilla a 2008, kuma ficewarsa a kaka mai zuwa babbar baraka ce ga kungiyar saboda takunkumin da FIFA ta kakaka ma ta na sayen ‘yan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI