La liga

Sevilla ta rike Barcelona 2 da 2

'Yan wasan Barcelona na jimame bayan Sevilla ta rama kwallaye 2
'Yan wasan Barcelona na jimame bayan Sevilla ta rama kwallaye 2 REUTERS

Barcelona ta yi barin maki biyu a jiya Assabar bayan Sevilla ta rike ta ci 2 da 2. Tun kafin aje hutun rabin lokaci Messi da Neymar suka jefawa Barcelona kwallaye biyu a raga amma bayan an dawo ne kuma Sevilla ta rama kwallayen.

Talla

Tuni Real Madrid ta lallasa Eibar ci 3 da 0, kuma yanzu maki biyu ne tsakanin Barcelona da ke jagorancin teburin La liga da kuma Real Madrid da ke biye mata a matsayi na biyu.

Cristiano Ronaldo yana cikin wadanda suka jefawa Real Madrid kwallo a raga, kuma yanzu kwallaye 49 ya zira a raga a La liga a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI