La liga

Barcelona ta casa Getafe

Messi da Neymar da Suarez na Barcelona
Messi da Neymar da Suarez na Barcelona REUTERS/Gustau Nacarino

Barcelona ta lallasa Getafe 6 da 0 gasar La liga da suka fafata a jiya Talata. kuma Messi da Suarez da Neymar ne suka yi ruwan kwallaye a wasan. Kwallaye 100 ‘yan wasan gaban guda uku suka jefa wa Barcelona a bana. Yanzu Barcelona ta ba Real Madrid tazarar maki 5 a teburin La liga, kafin Madrid ta buga wasanta a yau da Almeria a Santiago Bernabeu.

Talla

Kwallaye biyu Messi da Suarez suka jefa a ragar Getafe yayin da Neymar da Xavi suka jefa sauran kwallayen a raga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI