wasanni

Blatter ya yi lahani ga martabar hukumar FIFA in ji Platini

Shugaban hukumar UEFA Michel Platini
Shugaban hukumar UEFA Michel Platini UEFA

Shugaban hukumar kwallon kafar nahiyar turai UEFA Michel Platini ya ce, shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Sepp Blatter, karya yake akan batun shirin Janye takararsa. Platini ya ce a wani taro da suka gudanar a birnin zurich blatter ya nuna furgaba rasa kujeransa, kuma ya sha cewa zai hakura da takarar amma yakasa cika alkawarin.

Talla

Platini ya ce idan har Blatter ya ci gaba da shugabantar Fifa, sahihanci da martabar hukumar zai gushe, sannan za ta rasa karfin fada a ji a harkar kwallo, Saboda yana gani cewar Blatter ya yi lahani ga martabar hukumar

Ranar Lahadi mai zuwa ne za a gudanar da zaben shugaban hukumar ta Fifa, kuma ana hasashen cewar Blatter ne zai lashe zaben karo na biyar a jere.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.