FIFA

‘Yan sanda sun abka wa Ofishin FIFA a Zurich

Shugaban FIFA Joseph Blatter
Shugaban FIFA Joseph Blatter Reuters

Rahotanni daga Switzerland sun ce Jami’an tsaro sun abkwa ofishin hukumar FIFA a Zurich tare da kwace wasu muhimmacin takardu. Wannan kuma na zuwa ne bayan an cafke wasu manyan Jami’an hukumar a yau Laraba.

Talla

An cafke wasu manyan Jami’an hukumar ne guda 6 kan batun rashawa, kuma Jaridar New York Times ta ruwaito cewa za a mika jami’an ne zuwa Amurka bayan an cafke su a wata babbar Otel a Zurich.

Zargin rashawa da ake wa Jami ‘an ya kai dalar Amurka Miliyan 100, kan badakar ba Qatar da Rasha damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya. Kuma an yi amfani da bankunan Amurka ne wajen shigar da kudaden.

Jeffray Webb mataimakin Shugaban FIFA yana cikin wadanda aka cafke, a cewar Jaridar New York Times.

Tun tuni kasar Amurka ta kaddamar da bincike akan FIFA, lamarin da ya sa wasu Jami'an FIFA suka kauracewa zuwa kasar.

Wannan dai babban kalubale ne ga shugaban hukumar Sepp Blatter wanda ke neman wa’adin shugabanci na biyar a zaben hukumar da za’a gudanar a ranar Juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.