wasanni

Platini ya dage akan Blatter ya yi murabus

Shugaban FIFA Joseph Blatter
Shugaban FIFA Joseph Blatter REUTERS/Arnd Wiegmann

Shugaban hukumar kwallon kafa nahiyar turai UEFA Michel Platini ya dage akan lallai Sepp Blatter ya sauka daga mukaminsa, duk da dai Blatter ya ki. lamarin da ya kai ga, Platini fitowa karara a gaban ‘yan Jaridu yana cewa kar mambobi hukumomin kwallon kafa a duniya su zabe Blatter a zaben da za’a gudanar gobe.

Talla

Paltini dai na gani cewa lokaci ya yi daya kamata Blatter ya ajiye mukaminsa, domin baiwa wasu dama, Inda ya duga Jifar Blatter da kaukasar suka dangane da mulkin sa a hukumar da kuma batun takarasa a yanzu, musamman batun rikicin daya dabaibaye ta.

Shima ma dai Greg Dyke, shugaban kwallon kafar ingila ya bukaci Blatter ya yi murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.