Zakarun Turai

Suarez ba zai hadu da Chiellini ba

Luis Suarez na Barcelona
Luis Suarez na Barcelona Photo: Reuters/Albert Gea

Kungiyar Juventus tace Giorgio Chiellini ba zai buga wasan karshe a gasar zakarun Turai ba wanda Luis Suarez ya ciza a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Brazil. A gobe Assabar ne za a yi karabkiya tsakanin Juventus da Barcelona a gasar zakarun Turai zagayen karshe.

Talla

Rashin Chiellini zai rage wa wasan armashi domin ‘yan kallo za su so su ga yadda zai yi karabkiya da Suarez a karon farko tun lokacin da ya dankara masa cizo a lokacin da Uruguay ke fafatawa da Italiya.

Barcelona da Juventus dai na harin lashe kofuna uku a bana a fafatawar da za su yi a birnin Berlin na Jamus.

Juventus na harin lashe kofin gasar ne karo na uku yayin da Barcelona ke harin lashe kofin karo na biyar.

Amma wannan ne karo na farko da Juventus ta kai zagayen karshe cikin shekaru 12.
Dukkanin kungiyoyin biyu sun lashe kofin Lig dinsu da kofin gida yayin da ya rage dayansu ya karbi kofin gasar zakarun Turai a gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI