La liga

An sauya ranakun da za a yi Clasico a Spain

El clásico tsakanin Barça da Real
El clásico tsakanin Barça da Real

Kafin soma gasar La liga a Spain, an sauya lokacin da za a yi fafatawar Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid saboda wasan ya yi karo da wasu wasannin a Turai.

Talla

A ranakun 21 ko 22 ga watan Nuwamba ne za a yi fafatawar Clasico ta farko a gidan Madrid Santiago Bernabeu, tsawon mako biyu ke nan aka kara a lokacin da aka tsara tun a farko.

A ranakun 9 ko 10 ga watan Afrilu ne za a sake fafatawa a Nou Camp gidan Barcelona.

An sauya lokacin wasannin na La liga ne saboda wasannin da Barcelona za ta buga a gasar lashe kofin zakarun duniya na kungiyoyin kwallon kafa da kuma wasannin gasar Copa del ray.

A ranar 21 ga watan Agusta ne dai za a soma La liga a bana

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.