Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Mourinho da Fabregas suka sa na koma Chelsea- Pedro

New Chelsea signing Pedro with team mate Fabregas
New Chelsea signing Pedro with team mate Fabregas Chelsea FC

Bayan Chelsea ta kammala cinikin Pedro Rodriguez daga Barcelona, Dan wasan ya bayyana cewa kocin Chelsea Jose Mourinho da Cesc Fabregas ne suka sa ya amince ya koma Chelsea, duk da cewa Manchester United ce ta fara nemansa.

Talla

Pedro ya ce Mourinho da Fabregas dukkaninsu sun kira shi ta wayar tarho, kafin kulla yarjejeniya tsakanin Chelsea da Barcelona.

Barcelona dai ta sayar wa Chelsea da Pedro ne akan akan kudi fam miliyan 21. Dan wasan ya sanya hannu kan kwantaragin shekaru 4

Dan wasan mai shekaru 28 ya lashe wa Barcelona kofin zakarun Turai guda uku tare da jefa kwallaye 99 a raga a haskawa 326. Pedro ya lashe la liga 5.

Pedro dai na cin zaman benci a Barcelona matakin da ya sa ya yanke hukuncin barin kungiyar zuwa Chlelsea saboda yadda Luis Enrique ke yawan amfani da Lionel Messi da Neymar da kuma Luis Suarez.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.