Isa ga babban shafi
FIFA

Blatter ya wanke kansa daga zargin rashawa

An watsa wa Blatter kudaden jabu
An watsa wa Blatter kudaden jabu REUTERS/Arnd Wiegmann
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 min

Shugaban FIFA Sepp Blatter a jiya litinin ya wanke kansa daga zargin cin hanci da rashawa tare da ikirarin cewa babu rashawa a hukumar kwallon kafa ta duniya da ya ke jagoranta.

Talla

Duk da badakalar rashawa da ta dabaibaye FIFA amma Blatter ya ce  ba hannunsa a ciki, yana mai cewa wasu gurbatattu ne suka bata wa FIFA suna.

Amurka dai na zargin manyan Jami’an FIFA guda 14, da karbar cin hancin kudi sama da dala Miliyan 150.

A watan Fabrairun badi ne Blatter zai yi murabus, bayan an sake zabensa wa’adi na biyar, inda wasu ke ganin babu yadda za a yi ya wanke kansa saboda karkashin jagorancinsa sunan FIFA ya baci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.