Zakarun Turai

Rooney ya ci kwallaye uku

Manchester United  ta doke Club Brugge ta Belgium da jimillar kwallaye 7 da 1
Manchester United ta doke Club Brugge ta Belgium da jimillar kwallaye 7 da 1 Reuters

Kwallaye uku Wayne Rooney ya jefa a ragar Club Brugge a jiya Laraba wanda ya taimakawa Manchester United samun wuri a gasar Zakarun Turai.

Talla

Manchester ta lallasa Club Brugge ci 4 da 0 a Belgium, jimillar kwallaye 7 da1 ke nan bayan ta doke ta 3-1 karawar farko.

Hakan na nuna Rooney mai lamba 10 ya farfado a yanzu wanda ya shafe wasanni 10 bai jefa wa Manchester United kwallo a raga ba.

Manchester a bana za ta nemi huce hushin bara da ba ta samu shiga gasar Zakarun Turai ba.

Lazio ta Italia kuma ta sha kashi ne a gidan Bayer Leverkusen ci 3 da 0, bayan a karawa ta farko ta samu nasara ci 1 da 0.

Monaco ba ta samu shiga gasar zakarun Turai duk da cewa a jiya Laraba ta doke Valencia 2 da 1 amma Valencia ce ta tsallake da jimillar kwallaye 4 da 3.

CSKA Moscow ma ta tsallake da jimillar kwallaye 4 da 3 akan Sporting Lisbon , Ahmed Musa na Najeriya ne ya jefa wa CSKA kwallonta na uku a raga bayan Duambia ya jefa kwallaye 2.

Bate Borisov ta sha da kyar ne a karawarta da Partizan Belgrade.

Malmo ma ta tsalle da jimillar kwallaye 4 da 3 akan Celtic ta Scotland.

A yau ne kuma za a hada kungiyoyin da zasu kara a rukunin farko a gasar zakarun Turai a Monaco. Kuma hukumar kwallon Turai UEFA za ta zabi gwarzon dan wasa tsakanin Messi na Barcelona da Cristiano Ronaldo na Real Madrid da kuma Luis Suarez na Barcelona.

Ana ganin hasashen dai a bana Messi ne zai lashe kyautar bayan ya lashe kofuna, da suka kunshi kofin zakarun Turai da La liga da Kings Cup da Super Cup na Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.