Kwallon Kafa

An sake hada Arsenal da Bayern rukuni guda

Rukunin Farko a gasar Zakarun Turai
Rukunin Farko a gasar Zakarun Turai REUTERS/Eric Gaillard

Hukumar UEFA da ke kula da kwallo a Turai ta hada kungiyoyin da za su kara da juna a rukunin farko a gasar Zakarun Turai. A hadin da aka yi a Monaco ana ganin Barcelona mai rike da kofin gasar da kuma Manchester United sun samu bagas

Talla

Rukunun A.

An hada Paris St-Germaine ne da Real Madrid da Shaktar Donetsk da Malmo.

Rukunun B

An hada PSV Eindhoven da Manchester United da CSKA Moscow da Wolfsburg.

A bara Manchester United bata samu shiga gasar ba, kuma wannan hadin ya yi wa kungiyar dadi.

Rukunin C

An hada Benfica da Atletico Madrid da Galatasaray da Astana.

Rukunin D

An hada Juventus da Manchester City da Sevilla da Burssia Monchengladbach. Ana ganin wannan rukunin ya fi zafi ganin cewa Juventus ce ta buga was an karshe da Barcelona sannan Sevilla ce ta lashe kofin Europa League.

Rukunin E

An hada Barcelona mai rike da kofin gasar da Bayern Leverkusen da Roma da Bate Barisov

Rukunin F

An hada Bayern Munich da Arsenal da Olympiakos da Dinamo Zagreb.

Sau biyu Bayern Munich na haduwa da Arsenal a irin wannan zagayen na farko a kakar 2012/2013 da kuma kakar 2013 /2014

Rukunin G

An hada Chelsea ne da FC Porto da Dynamo Kiev da Maccabi Tel-Aviv.

Rukunin H

An hada Zenith Saint Petersburg da Valencia da Lyon da kuma Gent.

A ranakun 15 ga watan Satumba ne za a fara kece raini a rukunin farko, sannan za a yi fafatawar karshe a watan Mayun badi a San Siro filin AC Milan ta Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.